Subscribe Now: Feed Icon

.

Najeriya ta farfado daga kwallo guda da 'yan Ethiopia suka jefa a ragarta, ta jefa nata har guda biyu, ta samu zarafin numfasawa a zagayen farko na wasan share fagen shiga gasar cin kofin duniya yau lahadi a birnin Addis Ababa a kasar Ethiopia.

Wannan nasara da ta zo ta kafar dan wasan Najeriya mai suna Emmanuel Emenike, tana nufin cewa Najeriya ta dauki babban mataki na zuwa gasar cin kofin duniya shekara mai zuwa a kasar Brazil.

Emenike, ya jefa kwallon na biyu cikin minti na 90 a dalilin bugun fenariti da alkalin wasa ya bayar saboida wani dan wasan Ethiopia ya kayar da dan wasan Najeriya a kofar ragar 'yan Ethiopiar.

Za a kara zagaye na biyu ranar 16 ga watan Nuwamba a birnin Calabar dake kudancin Najeriya.

Kafin wannan bugun fenariti, Emenike ya jefa kwallon Najeriya na farko a minti na 67 da fara wasan, ya rama wa kasarsa ci dayan da aka yi mata tun kafin nan.

A dalilin wannan nasara da ta samu, yanzu kusan duk masu fashin bakin kwallo sun fara hasashen cewa Najeriya ce zata haye zuwa Brazil, abinda zai kawo karshen watanni 18 da 'yan wasan kasar Ethiopia suka yi su na bayar da mamaki a wasannin da aka yi na share fagen zuwa gasar cin kofin duniyar.

A sauran wasannin na yau da aka yi a Afirka, Burkina Faso ta doke Aljeriya da ci 3 da 2; Ivory Coast kuma ta doke Senegal da ci 3 da 1, duk a jiya asabar.

A yanzu haka da ake rubuta wannan labarin, Kamaru da Tunisiya su na gwabzawa, sun tafi hutun rabin lokaci, amma babu wadda ta jefa kwallo a raga har yanzu.

Ana cece-kuce game da nasarar Burkina Faso a kan Algeria daci uku da biyu a wasan neman gurbin zuwa gasar cin kofin duniya da suka buga a Ouagadougou.
Sau biyu Algeria na farke kwalo amma a dai dai lokacin da ake wasa 2- 2, sai alkalin wasa ya baiwa Burkina Faso bugun fenariti abinda ya baiwa tawagar galaba a kan 'yan
Algeria.
Da dama na ganin matakin a matsayin ya yi tsauri saboda wasu na ganin dan wasan Algeria Belkalem ya taba kwallon da kafada ne.
'Yan Algeria sun yi bore bayan wasan bisa abinda suka bayyana a matsayin rashin adalci.



Brazil 2014: Sakamakon wasanni a Turai
Wasu daga cikin kasashen Turai sun soma hangen tsallakewa zuwa gasar kwallon kofin duniya da Brazil za ta dauki bakunci a shekara ta 2014.
13.10.13
Rukunin A:
Croatia 1-2 Belgium
Wales 1-0 Macedonia 
Rukunin B:
Armenia 2-1 Bulgaria
Malta 1-4 Czech Rep.
Denmark 2-2 Italy
Rukunin C:
Faroe Islands 1-1 Kazakhstan
Jamus 3-0 R. of Ireland
Sweden 2-1 Austria
Rukunin D:
Andorra 0-4 Romania
Estonia 0-2 Turkey
Netherlands 8-1 Hungary
Rukunin E:
Albania 1-2 Switzerland
Iceland 2-0 Cyprus
Slovenia 3-0 Norway
Rukunin F:
Azerbaijan 2-0 Northern Ireland
Luxembourg 0-4 Rasha
Portugal 1-1 Israel
Rukunin G:
Lithuania 2-0 Latvia
Bosnia-Herzegovina 4-1 Liechtenstein
Greece 1-0 Slovakia
Rukunin H:
Moldova 3-0 San Marino
Ukraine 1-0 Poland
England 4-1 Montenegro
Rukunin I:
Spain 2-1 Belarus




Jordi Alba zai yi jinyar makonni 6
Dan kwallon Barcelona Jordi Alba zai yi jinyar makonni shida, sakamakon rauni da ya ji a cinyarsa.
Dan kwallon mai 24 ya soma murmurewa daga wani raunin kafin yaji sabon rauni.Barca ta na matsayi na daya a teburin La-Liga, bayan da ta lashe wasanni takwas a jere, tana kuma da banbancin yawan kwallaye tsakaninta da Atletico Madrid.Kawo 'yan kwallon Barcelona biyu Javier Mascherano, mai shekaru 29, da Carlos Puyol, mai shekaru 35, sun warke daga raunin da suka samu.Mascherano ya sami rauni a wasan da suka lashe Real Sociedad daci 4-1, shi kuwa Puyol ya fara jinya tun a Maris da gwiwarsa ta hana masa kwallo.


Brazil world cup qualifiers
Tunisia da kamaru sun tashi babu ci
Kasashen Belgium da Jermus da Colombia da Switzerland sun samu tikitin zuwa kofin duniya da Brazil za ta karbi bakunci 2014.
Kasashe 32, har da mai masaukin baki Brazil, za a raba zuwa rukunnai takwas da zasu kunshi kasashe hudu a kowanne rukunni da za a fidda ranar 6 Disemba a Costa do Sauipe da ke Bahia.Sauran kasashen da suka samu tikiti sun hada da Australia da Iran da Japan da South Korea da Costa Rica da Amurka. Sai Argentina da Colombia da su ma suka samu gurbi.A nahiyar Africa da sauran wasanni da ake sa ran kasashe biyar za su wakilce ta,
Tunisia vs Camaru

Tunisia da kamaru sun tashi babu ci
Tunisia da Kamaru sun barar da damar da suka samu a wasan farko na neman gurbin shiga kofin duniya inda suka tashi babu ci a filin wasa na Rades dake Tunis.
Tunisia ta kai hare-hare zafafa, amma golan Kamaru Charles Itandje ya sa kaimi bai yadda kwallo ta shiga raga ba.Saura kiris Kamaru ta jefa kwallo a ragar Tunisia, amma dama ta kwace mata lokacin da dan wasanta Pierre Webo ya hambari kwallo da kirjinsa, kuma tsakaninta da fadawa raga yadi biyar ya rage.Kamaru ta kusan samun Fenariti daf da tashi lokacin da Sameh Derbaly ya sa hannu.
Za su kara a wasa na biyu, inda za a raba gardama ranar 17 ga watan Nuwamba a Yaounden Kamaru



Paul Pogba

Juventus na kokarin sayar da Pogba

Juventus ta ce za ta sayar da, Paul Pogba, saboda karancin kudi da take fama a da shi.Shugaban kungiyar, Andrea Agnelli, ya ce abu ne mai wahala a ki sayar da Pogba, tsohon dan wasan Manchester United mai shekaru 20, idan har wata kungiya ta taya shi da daraja.Ya kara da cewa "abu ne mai wahala mu rike dan wasan domin ba mu da kudin da za mu rika biyansa"Pogba ya koma Juventus a watan Yuli a shekara ta 2012, bayan ya ki amincewa da yarjejeniyar da United ta nemi ya yi, ya buga wasanni 47 ya jefa kwallaye 7.

 

 Achchakir ya nemi sassauci daga FIFA

Dan kwallon Morocco, Abderrahim Achchakir ya bukaci FIFA ta dage masa dokar hana shi kwallo na shekara daya da ta dora masa sakamakon cin zarafin alkalin wasa da ya yi.Kotun daukaka kara ta wasanni ta tsaida ranar sauraron karar ranar 5 ga watan Nuwamba.Achchakir ya nemi cin zarafin alkalin wasa Helder Martins de Carvalho, nan take ya bashi jan kati a wasan da aka casa su daci 3-1 a Tanzaniya a watan Maris.FIFA ta kuma ci tararsa dalar Amurka 11,000.Dan kwallon dake bugawa FAR Rabat mai shekaru 26, zai dawo kwallo 13 ga watan Mayu, kuma bazai buga karawa da kungiyarsa zata buga a kofin zakarun nahiyar Afrika.

 

Jordi Alba zai yi jinyar makwanni 6

Dan kwallon Barcelona Jordi Alba zai yi jinyar makwanni shida, sakamakon rauni da yaji a cinyarsa.Dan kwallon mai 24 ya soma murmurewa daga wani raunin kafin yaji sabon rauni.Barca ta na matsayi na daya a teburin La-Liga, bayan da ta lashe wasanni takwas a jere, tana kuma da banbancin yawan kwallaye tsakaninta da Atletico Madrid.Kawo 'yan kwallon Barcelona biyu Javier Mascherano, mai shekaru 29, da Carlos Puyol, mai shekaru 35, sun warke daga raunin da suka samu.Mascherano ya sami rauni a wasan da suka lashe Real Sociedad daci 4-1, shi kuwa Puyol ya fara jinya tun a Maris da gwiwarsa ta hana masa kwallo.

 

 

Juventus na kokarin sayar da Pogba

Juventus ta ce za ta sayar da, Paul Pogba, saboda karancin kudi da take fama a da shi.
Shugaban kungiyar, Andrea Agnelli, ya ce abu ne mai wahala a ki sayar da Pogba, tsohon dan wasan Manchester United mai shekaru 20, idan har wata kungiya ta taya shi da daraja.
Ya kara da cewa "abu ne mai wahala mu rike dan wasan domin ba mu da kudin da za mu rika biyansa"
Pogba ya koma Juventus a watan Yuli a shekara ta 2012, bayan ya ki amincewa da yarjejeniyar da United ta nemi ya yi, ya buga wasanni 47 ya jefa kwallaye 7. 


Jose Mourinho chelsea
Kocin Chelsea Jose Mourinho ya ce yayi farinciki da Chelsea take cikin hudun farko a teburin premier, lokacin da aka tafi hutun makonni biyu.
Kwallayen da Eden Hazard da Willian suka zura a karshen lokaci, sun baiwa Chelsea damar lashe Norwich City 3-1 ranar Lahadi, wanda shi ne wasan farko da kungiyar ta samu nasara a waje a kofin Premier ta bana.Chelsea ta na matsayi na uku a teburin Premier, inda mai matsayi na daya ta tsere mata da maki biyu.Mourinho yace"An tafi hutun wasanni kuma kasancewarmu a saman tebur abu ne mai muhimmanci, kuma burinmu kenan,"

lazio president latito
Ba zan sayar da Lazio ba —Lotito
Shugaban kungiyar Lazio Claudio Lotito, ya ce ba zai sayar da kungiyar ba, duk da tayin da masu sayen hannun jarin kungiyar ke yi.
Tuni aka sayar da Roma, yayin da shugaban Inter Massimo Morrati, yake kokarin sayar da kungiyar ga dan kasar Indonesia Erick Thohir, gasar kwallo a Italy, ita ma ta bi sahun sauran wasannin Turai.Lotito ya jaddada cewar ba zai bi sawun sauran kungiyoyin ba, kuma ba zai yi wasa da jarinsa da ya sa a kungiyar ba.Mai shekarun haihuwa 56 ya mallaki kungiyar a shekara ta 2004, ko da yake ana matsa masa da ya canja salon juya kungiyar, amma ya ce zai ci gaba da jagorantar kungiyar.



Ambrose ya sabunta kwangilarsa a Celtic
Dan kwallon Celtic Efe Ambrose, ya amince da sabuwar yarjejeniyar shekaru hudu tare da zakarun kwallon Scotland.
Dan Najeriya mai shekaru 24, ya hade da Celtic ne a watan Agustan bara bayan ya bar Ashdod daga Isra'ila.A sabuwar yarjejeniyar zai ci gaba da kasancewa tare da kulob din har zuwa shekara ta 2017.Ambrose ya shaidawa shafin intanet ta Celtic cewar "Ina jin dadin kasancewa na tare da Celtic kuma ian farincikin tsawaita zama na tare dasu".




Wenger ya soki Wilshere kan sigari
Manajan Arsenal Arsene Wenger, ya bayyana cewar ba zai
 yadda da dabi'ar Jack Wilshere ta shan sigari ba.
A cewar kocin, zai fuskanci Wilshere gaba da gaba don su tattauna batun.A ranar Alhamis da safe ne aka dauki hoton Wilshere yana fitowa daga wata mashaya a London yana bukan sigari.Lamarin ya faru ne a daren ranar da Arsenal ta lallasa Napoli daci biyu da nema, amma ba a soma wasan da Wilshere ba.Wenger yace "sam ban yadda da wannan dabi'ar ba, ban san abinda ya faru ba, amma zan tattauna dashi".



No comments:

Post a Comment