Subscribe Now: Feed Icon

VOA





Jarumin Fina-Finan Hausa, Ali Nuhu
Ali Nuhu Ya Ce Masu Satar Fasaha Na Kawo Nak'asu
WASHINGTON, DC — Idan ku na biye da mu kun ji hirar Halima Djimrao kashi-kashi da shahararren dan wasan fina-finan Najeriya, Ali Nuhu wanda a kwanakin baya can ya zo nan Amurka ya karbi wata lambar girma da karramawa a fannin aikin shi na yin fina-finan Hausa da aka yi bikin bayarwa a birnin New York. A karashen hirar Ali Nuhu ya ce kasuwar fina-finan Hausa wane Najeriya, ta bunkasa har a kasashen yammacin Afirka kamar su Nijer da Ghana da Kamaru. Daga nan sai Halima Djimrao ta kada baki ta ce da Ali Nuhu, kowace irin kasuwa idan ta bunkasa ta gawurta, akwai wasu matsalolin da take tafe da su wadanda sai an yi da gaske a yi maganin su, sannan ta tambaye shi ko su ma a sana'ar su suna fuskantar irin wadannan matsaloli musamman ma a kasuwannin sayar da fina-finai?



Shugaba Goodluck Jonathan ya halarci Taron Koli Na Tattalin Arzikin Najeriya (NESG) a Abuja ranar 3 ga watan Satumba.

Taron Kasa Na Iya Kara Rarraba Kawuna: Sen Maccido
WASHINGTON, DC — Shugaban kwamitin kasafin kudi a majalisar dattijan Najeriya Ahmed Muhammad Maccido ya bayyana cewa, bai ga amfanin taron tuntuba na kasa da ake shirin yi a Najeriya ba.Saneta Maccido yace idan ba a yi hankali ba taron yana iya kara rarrabuwar kawuna a maimakon cimma manufar da ake tsammani. Bisa ga cewarshi, wadansu suna iya zuwa su kasa kai zuciya nisa a maimakon gyara su rika zagin juna.

No comments:

Post a Comment