Subscribe Now: Feed Icon

Friday, 4 October 2013

<

Image cap
Hukumomi a Nigeria za su kwace fasfo na diplomasiyya da kuma na jami'ai daga hannun tsofaffin jami'an gwamnati.
Hukumar kula da shige-da-fice ta kasar, NIS ce a cikin wata sanarwa ta bayyana haka inda ta ce matakin ya shafi tsofaffin gwamnoni da sanatoci da ministoci da wasu mutanen da suka taba rike manyan mukamai a gwamnati.
Sanarwar daga shugaban hukumar, Martin Abeshi ta ce duk wanda ya ki bin wannan umurnin za a dauki mataki a kan sa a filin jirgin sama.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsa za ta sake nazarin ofisoshin huldar jakadancinta da ke kasashen waje domin tantance wadanda suka fi muhimmanci don ci gaba da amfani da su.
Shugaban ya ce nan ba da jimawa ba za a kafa kwamiti na musamman domin yin aikin tantancewar ta yadda za a daga martabar ofisoshin jakadancin don su yi aiki yadda ya kamata.
Shugaba Buhari ya yi wannan furuci ne bayan da babban Sakatare a ma'aikatar kula da hulda da kasashen waje na kasar ya yiwa shugaban jawabi akan ayyukan ma'aikatarsa.


Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na biyu

Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na biyu ya yi kira ga jama'ar Jihar da kada su bari harin da aka kai ranar juma'a ya hana su gudanar da harkokinsu na yau-da-kullum.

Sarkin na jawabi ne a lokacin da tsohon shugaban Nigeria Janar Muhammadu Buhari ya kai masa ziyarar jaje.
Sarkin yace:" bayan addu'o'i da akeyi, a daure, a cigaba da harkoki na yau da kullum da mu'amaloli da aka saba amma tare da yin hattara".
Sarkin dai har sai da ya zubar da hawaye a lokacin da yake jawabi.
A jiya ne sarkin ya katse aikin umra da ya keyi a Saudiyya, kuma bayan ya dawo shine yayi limanci a masallacin da aka kai harin a lokacin sallar Magaruba.
Sama da mutane dari ne suka a mutu a harin na ranar Juma'a.
Wasu dadama kuma da suka samu raunuka a harin na kwance a asibiti yanzu haka.
Shaidu sun ce maharan sun tada bama-bamai ne a masallacin bayan an tada sallah.
Sun bada labarin harbe-harbe da wasu 'yan bindiga su ka yi bayan bama-bama sun tashi.
Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan ya yi Allah wadai da harin, ya kuma bayanashi da cewa wani aikin rashin imani ne.Ya kuma sha alwashin gano wadanda suka kai harinSarkin na jawabi ne a lokacin da tsohon shugaban Nigeria Janar Muhammadu Buhari ya kai masa ziyarar jaje.Sarkin yace:" bayan addu'o'i da akeyi, a daure, a cigaba da harkoki na yau da kullum da mu'amaloli da aka saba amma tare da yin hattara".Sarkin dai har sai da ya zubar da hawaye a lokacin da yake jawabi.A jiya ne sarkin ya katse aikin umra da ya keyi a Saudiyya, kuma bayan ya dawo shine yayi limanci a masallacin da aka kai harin a lokacin sallar Magaruba.Sama da mutane dari ne suka a mutu a harin na ranar Juma'a.Wasu dadama kuma da suka samu raunuka a harin na kwance a asibiti yanzu haka.Shaidu sun ce maharan sun tada bama-bamai ne a masallacin bayan an tada sallah.Sun bada labarin harbe-harbe da wasu 'yan bindiga su ka yi bayan bama-bama sun tashi.Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan ya yi Allah wadai da harin, ya kuma bayanashi da cewa wani aikin rashin imani ne.Ya kuma sha alwashin gano wadanda suka kai harin
Sarkin na jawabi ne a lokacin da tsohon shugaban Nigeria Janar Muhammadu Buhari ya kai masa ziyarar jaje.Sarkin yace:" bayan addu'o'i da akeyi, a daure, a cigaba da harkoki na yau da kullum da mu'amaloli da aka saba amma tare da yin hattara".Sarkin dai har sai da ya zubar da hawaye a lokacin da yake jawabi.A jiya ne sarkin ya katse aikin umra da ya keyi a Saudiyya, kuma bayan ya dawo shine yayi limanci a masallacin da aka kai harin a lokacin sallar Magaruba.Sama da mutane dari ne suka a mutu a harin na ranar Juma'a.Wasu dadama kuma da suka samu raunuka a harin na kwance a asibiti yanzu haka.Shaidu sun ce maharan sun tada bama-bamai ne a masallacin bayan an tada sallah.Sun bada labarin harbe-harbe da wasu 'yan bindiga su ka yi bayan bama-bama sun tashi.

Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan ya yi Allah wadai da harin, ya kuma bayanashi da cewa wani aikin rashin imani ne.Ya kuma sha alwashin gano wadanda suka kai harin



Gwamna Jang na Jihar Plateau

Rahotanni daga jihar Filato a Nijeriya sun ce jijiyoyin wuya na kara tashi dangane da matsayin da aka ce gwamnan jihar, Jonah Jang, ya dauka na gabatar da wani dan siyasa daga zuri'arsa a matsayin wanda zai gaje shi a matsayin gwamna a inuwar jam'iyyar PDP a zabukan dake tafe.Wannan yunkuri na gwamna dai,na neman rarraba kan jama'ar jihar ta Filato, wadda ke yawan fama da rigingimu.To sai dai gwamnan ya ce ai ba laifi ba ne idan ya nuna wanda yake so ya gaje shi, ko da kuwa dansa ne na cikinsa, amma hakan ba yana nufin an hana sauran 'yan takara shiga zabe ba ne.'yan siyasar jihar dai sun ce, kama-karya gwamnan ke neman yi musu, kuma ba za su taba amincewa da haka ba.


Iraqi ta yi watsi da gwamnatin hadin kai

Firai Ministan Iraqi Nouri al-Maliki ya yi watsi da kiraye-kirayen da ake yi masa na kafa gwamnatin hadin kan kasa.
Kasashen duniya ne ke bukatar a yi hakan domin a kawo karshen hare-haren da mayaka 'yan sunni ke kai wa a kasar.
A wani jawabi na mako-mako da yake gabatarwa ta gidan Talabijin a kasar, Mr. Maliki ya ce kiraye-kirayen tamkar juyin mulki ne ga kundin tsarin mulki da kuma tsarin siyasar kasar.
Ya ce hadarin da ke tattare da kiraye-kirayen da ake yi na kafa gwamnatin ceton kasa, ba wani boyayyen abu bane ga dukkan 'yan Iraqi.
A bangare daya kuma, Sakataren tsaron Amurka ya ce masu ba da shawara na sojin Amurka da aka tura domin taimaka wa sojojin Iraqi sun fara aiki.




Akalla mutane 12 ne suka rasa rayukansu a harin bam din da aka kai Banex Plaza a Wuse II da ke Abuja babban birnin Nigeria.
Haka kuma wasu mutanen da dama suka samu raunuka, yayin da masu aikin gaggawa ke ci gaba da ayyukan ceto.
Harin dai ya auku ne a lokacin da mutane ke hada-hada a rukunin shagunan na Banex.
Wadanda suka shaida lamarin sun ce sun ji karar fahewar wani abu kuma sun ga mutane na barin wurin da jini a jikinsu.




India: Mutane 89 sun mutu a turmutsitsi
'Yan sanda a India sun ce akalla mutane tamanin da tara ne suka rasu yayin turmutsitsi a wajen wani bikin ibadar 'yan Hindu da ake yi shekara shekara.
Lamarin ya faru ne lokacin da dubban masu ibadar suke kokarin tsallaka wata 'yar ƙaramar gada zuwa wurin ibadar dake Madhya Pradesh.
'Yan sanda sun ce, lamarin ya faru ne yayin da ake yada jita-jitar cewa, gadar zata rufta.
Wasu mutanen an tattake su ne wasu kuma suka sun nutse ne a ruwa.







Aikin taimakon jin kai na Red Cross
An sace ma'aikatan Red Cross a Syria
Kungiyar agaji ta duniya Red Cross ta ce an sace ma'aikatanta su bakwai a arewa maso yammacin Syria.Wata mai magana da yawun kungiyar a Damascus Rima Kamal ta shaidawa BBC cewa ma'aikatan kungiyar su shidda da kuma wani ma'aiakacin sa kai a kungiyar agaji ta Red Crescent na Syria an ritsa su da bakin bindiga aka kuma yi awon gaba da su a kusa da garin Saraqeb a gundumar Idlib.Ta ce tawagar ma'aikatan suna kan hanyar su ce ta komawa Damascus a yau a motarsu da aka zana tambarin Red Cross balobalo a jikinta.

John Boehner, Kakakin majalisar wakilan Amurka
'Yan Republican sun yi tayin mafita a dambarwar kasafin kudin Amurka
A Amurka, 'yan jam'iyyar Republican sun bada shawarar a kara yawan kudaden bashin da gwamnati za ta iya karbowa, na wucin gadi, domin gudun kada ta kasa biyan basusukan da ake binta.
Kakakin majalisar wakilai, John Boehner, ya ce zai aiwatar da matakin, in har shugaba Obama ya yarda a kara sasantawa a kan kasafin kudin kasar, wanda takaddamar da ake a kansa ta sa aka rufe wasu ma'aikatun gwamnati, a kwanaki goman da suka wuce.A cewar kakakin fadar White House, Jay Carney, mista Obama zai duba yiwuwar sa hannu a kan yarjajeniya ta dan lokaci:Ya ce, "za mu ga irin tayin da majalisar wakilai inda 'yan Republican ke da rinjaye ta yi tukuna, kafin mu yanke hukunci.Nan gaba manyan jam'iyyar Republican za su gana da shugaba Obama.Shugabar asusun bada lamunin IMF, Christine Lagarde, ta yi gargadin cewa, rashin tabbas game da kasafin kudaden Amirka, zai iya yin babbar illa ga tattalin arzikin Amirkan da kuma na sauran kasashen duniya.Ta ce, IMF bai tsoma baki a rikicin siyasar Amirkar ba.




kasashen Iran da Iraki sun yi masayar Gawawwakin dakarunsu a yakin da kasashen 2 suka gwabza a 1980-1988

kasashen Iran da Iraki sun yi masayar Gawawwakin dakarunsu a yakin da kasashen 2 suka gwabza a 1980-1988 
Kasahen Iran da Iraki a yau talata sun yi masayar gawawwakin sojoji 111 da aka kashe a lokacin yakin da kasashen 2 suka gwabza a 1980 zuwa 1988, kamar yadda kungiyar bayar da agajin jinkai ta Croix-Rouge da kuma ma’aikatar ministan kare hakkin dan adam ta kasar Iraki suka sanar.Sanarwar ta bayyana cewa, sauran gawawwakin dakarun kasar Iran 98 da na Iraki 13 da suka kwanta damar a yakin shekaru 8 da kasashen biyu suka gwabza a yau talata ne, aka yi masayarsu a kan hanyar Chalamja kusa da Bassora na kasar Iraki, a karkashin sa idon kungiyar bayar da agajin jinkan ta Croix rouge international.Masayar gawawwakin ya hadu da wasu shagulgula da suka samu halartar wakili ma’aikatar ministan kare hakkin dan adam ta kasar Iraki a Basora, Mahdi al Tamimi da kuma wani janar din sojan kasar Iran, Mohamed Bagir Zada.
 


Wasu dauke da akwatin wani mamaci
An kaiwa masu aikin Polio hari a Pakistan
Akalla mutane biyu cikinsu har da wani jami'in dan sanda, sun rasa rayukansu a wani harin bam din da aka kai kusa da ofishin yaki da cutar shan inna ko Polio, a Penshawar dake Pakistan.
Yayin da wasu mutane 12 suka jikkata, kuma rahotanni sun ce mafi yawansu 'yan sanda ne, amma an nuna wata yarinyar da ta ji rauni a hoton bidiyon harin.Rahotanni sun ce tawagar dake cikin motar da aka kaiwa harin, na rakiyar ma'aikatan polio ne domin basu kariya.Masu ta da kayar baya dai sun kai hare-hare a kan ma'aikatan rigakafin shan inna, tare da haramta ayyukansu a wasu yankunan kasar, lamarin da ya sa dole ba a samu yiwa dubban yara rigakafin ba.



Joe Hart Manchester City
Na kusa na ajiye Hart — Pellegrini
Kocin Manchester City Manuel Pellegrini, ya so ya ajiye mai tsaron ragar England Joe Hart, a karawar da suka yi da Everton.
Hart, da ake zargin ya yi kura-kurai a satuttukan baya, an zura masa kwallo ta hannun Romelu Lukaku kafin daga baya su lashe wasa da ci 3-1.Kwallon da aka zura masa ta sa shakku game da tashen da mai tsaron ragar ke yi .Pellegrini ya ce "ya kamata a samu amincewata da ta 'yan wasa da magoya bayan kungiyar"







Harin Gwoza
Mazauna garin Gwoza na zaman dar-dar
A Najeriya, al'ummar karamar hukumar Gwoza da ke jihar Borno a arewa maso gabashin kasar sun koka game da zaman dar-dar da suke ciki sakamakon yawan hari da suka ce 'yan kungiyar jama'atu ahli sunna lidda'awati waljihad na kai musu.
Mazauna garin sun shaidawa BBC cewa 'yan kungiyar ta Boko haram sun kona makarantu, baya ga tare mutane da suke yi kuma akan hanya.
Wani mazaunin garin da ya gudu ya kuma nemi a sakaya sunan sa, ya shaidawa BBC cewa, ko a ranar asabar din da ta gabata wasu 'yan bindiga sun tare hanya inda suka tsaya adai-dai wani kauye mai suna Kirawa suka tare mutane idan sun ji kai dan Gwoza ne ko Bama sai su yanka ka.
Mutumin ya bayyana cewa, yanzu haka mutanen garin musamman matasa duk sun gudu.
Wannan dai ba shi ne karon farko da aka taba kai hari garin na Gwoza ba, ko a watannin baya ma wasu 'yan bindiga sun kai hari kan gidan yarin garin inda suka kubutar da mutane da dama wadanda ke zaman gidan kaso.
Kazalika a kwanan baya ma an kai hari a Gujba da ke jihar Yobe a kan makaranta inda aka kashe dalibai kusan hamsin aka kuma kona azuzuwa.



sojojin Amurka
An kama wani jagoran al-Qaeda a Libya
Hukumomin Amurka sun ce sun kama wani jagoran kungiyar al-Qaeda na Libya.
An kama shugaban ne mai suna Anas al-Libi a Tripoli.Ana neman mutumin mai shekara 49 bisa zargin hannu a harin da aka kai kan ofisoshin jakadancin Amurka a gabashin Afrika a 1998.Daman an sanya ladan dala miliyan biyar ga duk wanda ya bayar da bayanan da zasu taimaka a kama shi.


Masu zanga-zanga a Iraki
An yi zanga-zangar kin jinin Piraministan Iraki
Dubun dubatar ‘yan sunni ne a kasar Iraki a yau juma’a suka gudanar da wata zanga-zangar neman murabus din Piraministan kasar dan Shi’a Nuri Al-maliki da suke zargi takurawa ‘yan sunni na kasar.


wasu jerin hare haren ta'addanci a kasuwar  Kadhimiya dake Bagdad, 8 février 2013.

 Mutane sama da 20 sun mutu a harin ta'addanci a kasar Iraki

Wani rugumutsin tashin Boma-bomai da aka samu a wata Kasuwa dake a yankin ‘yan Shi’a a kasar Iraqi yayi sanadin mutuwar akalla mutum 29.Hakama wannan harin da ka kai a Kasuwa, yayi sanadin jikkatar wasu mutane 70.Da misalin karfe 9 na safiya ne dai aka kai wannan harin da ya hallaka mutum 16 kai tsaye, wasu 43 suka ji rauni.

Wata mace take rike da katin kuri'a a wata rumfar zabe a Niamey,babban birnin Nijar.
Jam'iyun Hamayya Sun Kulla Kawance a Nijar
A yau ne wadansu jam’iyyun hamayya 19 cikinsu har da uku mafiya karfi a kasar suka kulla kawancen gwagwarmayar kwatar mulki a jamhuriyar. Wannan kawancen yazo ne ‘yan watanni bayan tsunduma da kasar tayi a cikin rudanin siyasa
.Burin da wannan kawancen yake neman cimma shine na abinda suka kira tsamo jamhuriyar daga cikin halin da gwamnatin da jamhuriya ta bakwai suka saka ta a ciki. Tare da kwato al’ummar ta jamhuriyar Nijar ta hanyar shirya gwaggwarmayar kwato iko ko kuma tankwaso da mahukumtan Nijar din da su dawo daga rakiyar korar fara a daji da suka ce gwamnatin Nijar tana yi yau sama da shekaru biyu da rabi.Dama dai an jima ana harsashen kulla kawance a tsakanin jam’iyu mafiya karfi a jamhuriyar Nijar tun ranar da jam’iyar PNDS Tarayya mai mulki a jamhuriyar tayiwa wadansu ‘ya’yan jam’iyun dauk daidai kuma ta sakasu cikin gwamnatin hadin kan kasa da shugaban kasar Issouf Mahammadu ya nada a cikin watan Agustan da ya gabata.


FIFA ta zabi Qatar ta dauki bakuncin gasar cin kofin duniya
FIFA za ta yi taro kan gasar Qatar
Hukumar kula da kwallon kafa ta duniya FIFA za ta yi wata ganawa a ranar Juma'a, domin tattauna yiwuwar dage gasar cin kofin kwallon kafa ta shekarar 2022 da aka shirya yi a Qatar, zuwa lokacin sanyi.
An kawo shawarar sauya lokacin gasar ne saboda tsananin zafin da ake yi a kasar lokacin bazara, sai dai ana fargabar hakan zai haddasa tsaiko ga wasannin kwallon kafa na cikin gida.Masu aiko da rahotanni sun ce da alamu za'a dauki lokaci mai tsawo ana tattaunawa, kafin amincewa a kan wata matsaya.Haka kuma hukumar za ta yi tsokaci game da zargin da aka yi na cin zarafin 'yan cirani na kasar Nepal, dake gina guraren wasan da za a yi gasar.Qatar ta kare kanta game da kare hakkin ma'aikata a kasar.


jagoran addini na Iran Ayatollah Ali Khamenei
Sabon yunkurin Iran na diplomasiyya
Jagoran addini na kasar Iran Ayatollah Ali Khamenei ya baiyana goyon bayan yunkurin diplomasiyyar kasar na baya bayan nan.
Sai dai kuma yace wasu abubuwan da suka faru a lokacin ziyarar da sabon shugaban kasar Hassan Rouhani ya kai domin halartar taron Majalisar Dinkin Duniya a makon da ya wuce basu dace ba.An ruwaito Ayatollah Khamenei yana cewa a shafinsa na Internet, har yanzu Iran na dari-dari da Amirkawa.Ya baiyana gwamnatin Amirka da cewa ba abar amincewa bace.


Shugaba Goodluck Jonathan ya halarci Taron Koli Na Tattalin Arzikin Najeriya (NESG) a Abuja ranar 3 ga watan Satumba.
Taron Kasa Na Iya Kara Rarraba Kawuna: Sen Maccido
WASHINGTON, DC — Shugaban kwamitin kasafin kudi a majalisar dattijan Najeriya Ahmed Muhammad Maccido ya bayyana cewa, bai ga amfanin taron tuntuba na kasa da ake shirin yi a Najeriya ba.Saneta Maccido yace idan ba a yi hankali ba taron yana iya kara rarrabuwar kawuna a maimakon cimma manufar da ake tsammani. Bisa ga cewarshi, wadansu suna iya zuwa su kasa kai zuciya nisa a maimakon gyara su rika zagin juna


Jirgin ruwan da ya nutse a tekun kusa da Lampedusa
Torokon teku na shafar ceto a Lampedusa
Rashin kyaun yanayi a tsibirin Lampedusa ya sa ma'aikatan ceto sun kasa komawa ayyukan da suka fara na tsamo gawarwakin bakin hauren nan da suka nutse a teku a farkon makon nan.
Tun a jiya, Juma'a da yamma ne aka fara fuskantar wannan matsala, wadda ta kawo cikas ga aikin.Ana fargabar cewa har yanzu akwai gawarwakin mutane dari biyu a cikin tekun.
wasu 'yan sandan majlisar dokokin Amurka na kallon motar matar da aka kashe ranar 3 ga watan oktoba
Ana Binciken Kisan Da Aka Yiwa Wata Mata
WASHINGTON, DC — Hukumomin kasar Amurka na ci gaba da kokarin gano dalilin da ya sa wata mata dauke da 'yar ta a cikin mota ta yi yunkurin kara motar ta, ta, da wani shingen tsaro a fadar shugaban kasa ta White House, wanda hakan ya sa 'yan sanda suka bi ta a guje da motocin su karshen ta suka harbe ta har lahira a kusa da majalisar dokokin Amurka.Mahaifiyar ta mai suna Idella  Carey ta ce sunan matar Miriam Carey kuma shekarun ta 34. Mahaifiyar ta shaidawa gidan talbijin din ABC cewa 'yar ta, ta yi fama da matsalar rashin lafiya mai nasaba da kunci da damuwa bayan haihuwar 'yar ta a cikin watan agustan da ya gabata, wadda da turanci a ke kira Postpartum Depression.Majiyoyin 'yan sanda sunce matar ta na da tarihin tabun hankali kuma a cikin kan ta,  ta na jin kamar shugaba Barack Obama ya na yi ma ta magana.'Yan majalisar dokoki da ma'aikatan majalisar sun yi awa daya a killace a wani daki a lokacin da abun ke faruwa a ranar alhamis, amma 'yan sanda sun ce babu wata barazanar da aka yiwa 'yan majalisar dokokin daga cikin ginin majalisar.Hukumomi sun ce jami'an 'yan sanda biyu sun ji ciwo kuma ana kyautata cewa za su samu sauki. Kuma ba sa jin cewa al'amarin ya na da nasaba da matsalar rufe wasu ma'aikatun gwamnatin da ake fama da ita yanzu haka a kasar Amurka.




zanga zangar kasar Masar
An kashe akalla mutane hudu a Masar
Akalla mutane hudu ne suka mutu sakamakon harbin bindiga a babban birnin Masar, Alkahira.
Inda jami'an tsaro suke dauki-ba-dadi da daruruwan magoya bayan kungiyar 'yan uwa musulmi.Masu zanga zangar dai na kokarin isa tsakiyar dandalin Tahrir ne cibiyar zanga zangar Masar.Su kuma jami'an tsaron ke kokarin hana su kai wa wurin ta hanyar amfani da hayaki mai sa hawaye tare da harbi.
A fadin kasar ta Masar an jikkata akalla mutane 40 kuma.


filin jirgin saman nijeriya
Maniyyata Hajji sun tsallake rijiya da baya
Wani jirgin sama dauke da maniyyata aikin hajji 'yan jirgin yawo, su kimanin dari hudu, ya yi saukar gaggawa a Sakkwato bayan tayoyinsa sun fashe.
Rahotanin da muka samu sun ce Jirgin na kamfanin Kabo ya tashi ne daga Kano.Kuma an sauki maniyyatan a wani babban Otal da ke birnin Sakkwato.



Lampedusa: An samu tsaiko a aikin ceto
Igiyar ruwa ta kawo cikas ga aikin ceton da ake yi na tsamo gawarwakin
 'yan ci-rani daga tekun Lampedusa na kasar Italiya.




'Yan Najeriya Da Nijar Zasu Ga Khusufin Rana
wamba, 2013 tun daga misalin Karfe 1:15pm na azahar za a fara ganin
 Khusufin Rana a fadin Najeriya da Nijar da sauran kasashen Afirk


Ana duba yara a karamin asibiti dake kauyen Bagega a jihar Zamfara ta arewa maso yammacin Najeriya.

An Kera Wata Na'urar Aikin Rigakafi
A Kasuwar baje koli ta kasa da kasa da ake yi a Abuja, an baje wata na'ura da zata taimaka wajen ayyukan kiwon lafiya.





Account ID: pub-1081887709407508